Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta Ingila tana shirin shiga cikin filin wasa na Parc des Princes yau talata a birnin Paris da abu guda a ran ta: yadda zata ceto kakar kwallonta ta bana a gasar cin kofin zakarun kulob kulob na Turai.
Kakar firimiya Lig ta Ingila a bana dai ba ta yi ma Chelsea dadi ba, duk da cewa ita ce ke rike da kofin a yanzu, tana can baya sosai, kuma idan ba wani ikon Allah ba, babu ta hanyar da zata iya sake komawa ga wannan babbar gasar kwallon kafa ta Turai a shekara mai zuwa. A zagaye na biyu na wannan gasa a bara, PSG ta cire Chelsea, ta wuce zuwa kwata fainal.
A yau, ‘yan wasan Chelsea suna Paris ba tare da kyaftin dinsu ba, watau John Terry, wanda ya ji rauni a wasan da kungiyar ta yi da Newcastle a karshen mako.
A wasan da suka yi da Newcastle, manajan Chelsea Guus Hiddink ya maye gurbin Terry da Baba Rahman, wanda bai kware a filin was aba. A yau talata ma, ana sa ran cewa abinda zai yi ke nan tun da Terry ba zai buga ba.
Dukkan ‘yan wasan baya na Chelsea zasu canja wuraren da suka saba tsayawa a fili kasancewar babu Terry. Chelsea dai zata fuskanci kungiyar PSG wadda ta lashe wasanni 20 daga cikin 22 da ta buga na baya bayan nan.