Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Likita Yayi Kuskure Wajen Yanke Harshen Jariri Mai Koshin Lafiya


Baby Cuddlers
Baby Cuddlers

Jennifer Melton, mahaifiya ga wani sabon jariri Nate, wannan jaririn an haifeshi lafiya lau, bayan kwanaki kadan da haihuwar jaririn, mahaifiyar yaron da mahifin shi sun dauki jaririn zuwa asibitin koyarwa na jami’ar tsakiya a garin Lebanon ta jihar Tennessee, a nan kasar Amurka, don ganin likita kamar yadda aka saba.

Bayan sun isa asibitin, masu taimakon likita, "Nurse"sun karbi jaririn suka shiga da shi cikin dakin tiyata, wanda akayima jaririn aiki a kasan halcen shi. Ashe dai wannan jaririn ba shine ya kamata a yima wannan aikin ba. Bayan wasu lokkuta kadan sai ga mataimakiyar likita ta fito tana ma mahaifiyar yaron bayanin yadda aikin ya kasance.

Ta gayamata cewar an yanke kasan halcen yaron, sannan aka dinke, hakan dai yasa mahaifiyar yaron cikin rudani, sai ta tambaye ta meyasa haka, koda dai aka duba sai aka gane cewar ashe anyi aiki akan wani jariri da bashi ne aka shiryar da za’a yima aikin ba. Likitan dai ya dauki laifin yin aiki bisa kuskure, iyayen yaron sun nuna damuwar su matuka, da cewar kada yaron ya samu matsalar rashin iya magana ko wani abu makamancin hakan, akan dalilin yanke mishi kasan halce da likitan yayi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG