Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD, Najeriya Sun Samu Sabanin Ra’ayi Kan Makomar ‘Yan Gudun Hijira


'Yan gudun hijira a sansanin Minawao dake arewa mai nisa a Kamaru
'Yan gudun hijira a sansanin Minawao dake arewa mai nisa a Kamaru

A ‘yan kwanakin nan hukumar dake kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, UNHCR, ta yi ikirarin cewa hukumomin Kamaru na tilastawa wasu ‘yan gudun hijrar Najeriya komawa gida, zargin da Najeriya ta musanta.

Hukumar dake kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, (UNHCR) ta zargi hukumomin Kamaru da cewa suna tilasatawa wasu ‘yan Najeriya dake samun mafaka a kasar komawa gida.

Akasarin ‘yan gudun hijirar sun fito ne daga garin Maiduguri dake Borno, jihar da ta fi fama da matsalar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriyar.

Wakiliyar hukumar dake kula da ‘yan gudun hijirar ta Majalisar Dinkin Duniya a yankin Yammacin Afirka, Madam Liz Ahau ce ta bayyana hakan a wani taro da aka gudanar na masu ruwa da tsaki kan makomar ‘yan gudun hijirar a Maiduguri.

Madam Ahua wacce ta yi magana da harsen Ingilishi a wajen taron, ta ce duk da cewa akwai wadanda suka koma gida domin gashin-kansu, har ila yau akwai wadanda aka turasasa masu komawa gidan.

Ta kuma bayyana cewa akwai bukatar a fito da irin wadannan matsaloli fili domin a kyautata dandantaka a tsakanin juna.

"Ba wai muna so mu haddasa tarzoma bane tsakanin kasashen biyu." Madam Ahua ta kara fada a jawabinta.

Sai dai yayin taron, shugaban hukumar shige-da-fice a jihar Borno, Alhaji Bello Jahun, ya musanta ikirarin na Madam Ahua.

“Batun tilastawa na komawa gida, ina so na fadu maku cewa babu wani abu kamar haka.” A cewar Bello wanda shi ma ya yi magana da harshen Ingilishi a taron.

Yayin shi ma da aka tuntube shi kan wannan batu, shugaban hukumar ba da agajin gaggawa a jihar Borno, Engineer Ahmed Satomi, ya ce babu kanshin gaskiya kan zancen tilasawa ‘yan gudun hijirar Najeriya komawa gida.

“A wannan satin da ya gabata sama da mutum 92,000 su ke Kamaru a Minawao Camp, wadanda an yi masu rijista kuma ba a tilastawa kowa ya koma gida ba.”

A watan Maris din wannan shekarar kasar ta Kamaru da Najeriya hade da hukumar ta UNHCR, suka rattaba hanu a wata yarjejeniyar shirin mayar da ‘yan gudun hijirar Najeriya zuwa gida - amma ga wadanda suka yi zabin hakan, inda aka amince za a mayar da su cikin mutunci.

Saurari rahoton wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda Biu domin jin karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG