Shi dai wannan dan takara da jam’iyyar PDP ta tsayar a matsayin dan takarar shugabancin karamar hukumar Agege, mai suna Injiniya Auwal Tahir Maude, wanda aka fi sani da ATM, yana samun cikakken goyon baya daga ‘yan kabilar yarbawa.
Da yake jawabi, dan takarar ya bayyana cewa daukacin ‘yan arewa mazauna wannan yanki na taka rawar gani wajan ba da cikakken hadin kai musamman wajen harkokin siyasa da sauran abubuwan da suka shafi zamantakewa.
Injiniya Auwal, ya kara da cewa akwai ‘yan kabilar yarbawa da dama dake mara masa baya domin a cewarsa zaman tare da Hausawa ‘yan arewa ke yi da ‘yan kabilar ta yarbawa ya sa sun zama tamkar tsintsiya madaurin ki daya.
Mr Femi Aloko, daya daga cikin mazauna yankin ya bayyana cewa yana daya daga cikin masu marawa bahaushe dan arewa baya domin kasancewar sa haifaffen karamar hukumar ne kuma yana amfani da duka harsuna uku wato yarbanci da hausa da kuma turanci, dan haka babu matsalar cudanya tsakanin su.
Domin karin bayani, saurari rahoton Babangida Jibrin a nan.
Facebook Forum