An wayi gari a Amurka cikin wani sabon makon da aka koma bakin aiki, bayan da aka yi fama da tashe-tashen hankula na tsawon mako guda, a lokacin da wasu ‘yan sanda biyu suka harbe wasu bakaken fata har lahira a jihohin Louisiana da Minnesota, tare da harbe wasu ‘yan sanda biyar suma har lahira da aka yi a birnin Dallas da ke jihar Texas, a wajen wata zangar zangar lumana ta jama’an da ke adawa da yadda ‘yan sanda ke muzgunwa bakaken fata.
‘Yan sanda a Dallas din sun ce wani dan bindiga mai suna Micah Xavier Johnson ya kitsa kai karin wasu munanan hare-hare, da za su ta da hankalin birnin.
Shugaban ‘yan sandan birnin Dallas, David Brown, ya ce, sun samu tabbacin cewa mutumin da ake zargin ya na da wani shirin kai hare-hare akan jami’an tsaro, wanda, a tunaninsa, kamar ramakon gayya ne akan ‘yan sanda da ke muzgunawa bakaken fata.
‘Yan sanda dai sun yi nasarar dakile shirin Johson ta hanyar yin amfani da wani bam da mutum-mutumi ya dasa a dakin ajiye motoci da Johnson ya fake.
Shugaban ‘yan sandan ya gayawa gidan talbijin na CNN cewa, daukan wannan mataki na dasa bam ta hanyar yin amfani da mutum-mutumin, ya zama dole domin a ceci rayukan jama’a.