Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Yau 'Yansandan Amurka Suka Fara Kashe Bakake Ba - Obama


Shugaba Obama yana jawabi akan 'yansandan kasarsa a Poland.
Shugaba Obama yana jawabi akan 'yansandan kasarsa a Poland.

Shugaban Amurka Barrack Obama ya fada cewa wannan ba shine karo na farkon da suka ga irin wannan harbin ba.

Shugaban yana wa ‘yan jarida tsokaci ne game da wani harbin da wasu suka bayyanna na ganganci da akayi wa wasu bakaken fata Amurkawa anan Amurka a cikin ‘yan kwanaki biyun da suka gabata.

Wannan harin dai ya sake tada wata alamar tambaya akan irin yadda ‘yan sanda ke wuce gona da iri wuri a aikin su musammam ga tsiraru.

Dansanda a Dallasa dake jihar Texas yana sa ido a wurin da bakake suka fi yawa a birnin
Dansanda a Dallasa dake jihar Texas yana sa ido a wurin da bakake suka fi yawa a birnin

Da sanyin safiyar yau Juma'a ne dai Obama yake wannan Magana, jim kadan da saukar sa Warsaw, Poland inda zai halarci taron NATO.

Yace yakamata duka Amurkawa su nuna damuwar su game da wannan aika-aikan na yadda ‘yan sanda suke harbin bakaken fata, wanda yake kara aukuwa.

Shugaba Obama ya kira wannan nuna tsananin banbanci musammam akan tsarin shari'ar kasar Amurka, yace wannan banbanci kuma kididdiga ya nuna cewa Amurkawa bakake da ‘yan Latino suna ganin banbanci daga wurin ‘yan sandan kasar.

Yace da zaran irin hakan ta faru, da yawan Amurkawa sukan rika jin cewa ana yi wa bakake haka ne sabo da launin jikin su, ba a daukar su daya da sauran jama'ar kasar farare ba, wannan abin kuma yana bata rai kwarai da gaske.

Yayinda yake jawabi a Poland sai gashi a biranen Dallas da Washington DC bakake na zanga zangar kin jinin 'yansandan. A Dallas ma 'yansanda goma aka harba kuma tuni uku daga cikinsu suka rigamu gidan gaskiya.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG