Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kashe Bakake da 'Yansanda Suka Yi Ya Haifar da Zanga-zanga A New York


Masu zanga-zanga a birnin New York dake Amurka
Masu zanga-zanga a birnin New York dake Amurka

Harbin da ‘yan sanda suka yi wa wasu bakaken fata a nan Amurka da yayi dalilin mutuwar wasu mutane biyu, yanzu haka ya haifar da zanga-zanga.

Daruruwan mutane ne suka yi maci zuwa dandalin TIME SQUARE dake birnin New York domin gudanar da zanga-zanga na nuna kyamar su akan kashe Philando Castile wanda aka yi a Minesota da kuma wanda aka yi wa Alton Sterling a Baton Rauge dake Louisiana.

Masu zanga-zangar suna tafe suna daga hannuwan su suna cewa a daina harbi kuma suna kira da a yi adalci ga Bakaken Amurkawan da ‘yansanda suka harbe.

Wannan kashe bakaken fatan har su biyu da a kayi cikin wannan satin ya tada wata alamar tambaya game da yadda ‘yansanda ke anfani da karfi fiye da kima musammam akan tsiraru bakake.

Daya daga cikin masu zanga-zangar a New York mai suna Michael Huston dan shekaru 20 yace bakin ciki da rashin daukar matakin da ba ayi yasa shi shiga cikin wannan zanga-zangar.

Yace wannan shi ake kira rashin sanin yakamata,Hustan yana Magana ne da kanfanin diilacin labarai na ASSOCIATED PRESS.

Yace ta yaya abubuwa zasu sake tunda ko ba ayi kome ba akan su.

XS
SM
MD
LG