Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalla-Dallar Bayanin Yadda Aka Kashe 'Yan Sanda 5 A Dallas


'Yan sanda tsaye a kofar dakin jinyar marasa lafiya na gaggawa a asibitin Jami'ar Baylor dake Dallas, Jumma'a Yuli 8, 2016
'Yan sanda tsaye a kofar dakin jinyar marasa lafiya na gaggawa a asibitin Jami'ar Baylor dake Dallas, Jumma'a Yuli 8, 2016

Kisan 'yan sandan ya samo asali daga wata zanga-zangar lumana da aka fara da karfe 7 na yammaci agogon Dallas, karfe 1 na dare agogon Najeriya

'Yan sanda da kafofin labarai a birnin Dallas a Jihar Texas, sun bayar da bayanin yadda aka yi kwanton-bauna ma jami'an 'yan sanda har aka kashe guda biyar daga cikinsu kamar haka:

Da karfe 7 agogon birnin, daruruwan masu zanga-zanga sun hallara a filin shakatawa na Belo Garden Park su na kiran da a yi garambawul ga tsarin ayyukan 'yan sanda, a bayan da wasu 'yan sanda fararen fata suka harbe bakaken fata biyu a Baton Rouge dake Jihar Louisiana da kuma St. Paul a Jihar Minnesota.

Da misalin karfe 7 da minti 16 na dare, 'yan zanga-zangar sun fara yin maci suna cewa "mun gaji, mun gaji" kamar yadda aka gani cikin bidiyo na 'yan sandan Dallas.

Da karfe 9 na dare, kafofin labarai da dama sun bayar da rahotannin cewa an ji karar harbe-harbe.

Da karfe 9 da minti 5 an ji karar harbe-harben bindigogi a wani hoton bidiyo, aka kuma ji 'yan sanda su na ta cewa ana bude mana wuta a kusa da inda wasu hanyoyi biyu suka hadu. An ga mutane sun tsorata su na ta gudu.

Da karfe 10 da minti 23, rundunar 'yan sandan Dallas ta fada ta shafukanta na intanet da sada zumunci cewa "da alamun wasu 'yan kwanton-bauna biyu" sun harbi 'yan sanda goma daga "rufin wani gini" lokacin zanga-zangar, suka kashe "'yan sanda 3, biyu kuma su na dakin tiyata, wasu uku suna kwance rai hannun Allah."

Da karfe 1 da minti 13 na dare, Rundunar 'yan sandan Dallas ta fada ta Twitter cewa "an kashe dan sanda na hudu."

Da karfe 1 da minti 27 na dare, rundunar 'yan sandan Dallas ta fada a shafukanta na sada zumunci zaratan 'yan sanda na runduynar SWAT sun kama wani wanda suka yi musanyar wuta da shi, kuma ana binciken wani kunshi da aka gani kusa da shi.

Da karfe 3 na dare, an bada rahoton mutuwar wani wanda yake musanyar wuta da 'yan sanda a garejin ajiye motoci na makarantar El Centro College.

Da karfe 4 da minti 3 na asuba, watau karfe 10 da minti na safiyar yau agogon Najeriya, rundunar 'yan sandan ta Dallas ta ce ba ta taba ganin dare mai munin wannan ba, jami'inta na 5 ya mutu.

XS
SM
MD
LG