Ya ce, "Mu na iya bullo da wata fiyayyar hanyar hulda da cudanya ko kuma mu sake komawa tsarin duniya mai cike da rarrabuwar kawuna, har mu kai ga tashe-tashen hankula irin na can baya bisa ga banbancin al'umma da kabila da jinsi da kuma addini," Ya cigaba da gaya ma Shugabannin kasashen duniya jiya Talata cewa, "Ina so in ba ku shawara yau cewa, mu cigaba da zurkuwa, kar mu koma baya."
Obama, wanda zai sauka daga mukamin Shugaban kasa a watan Janairu, ya tabo cigaban da aka samu a tsawon shekaru 8 na wa'adinsa, ciki har da rage tsabar talauci, da warware takaddamar shirin nukiliyar Iran, da maido da hulda da kasar Cuba, da kuma cimma yarjajjeniyar kasa da kasa kan dumamar yanayi.
"Wannan al'amari ne mai matukar muhimmanci, ya haifar da da mai ido a rayuwar mutanenmu kuma ba don mun hada kai ba, da hakan bai faru ba," a cewar Obama.
To amma ya yi gargadin cewa har yanzu akwai matsala sosai a matakin kasa da kasa, wanda hakan ke haddasa kwararar 'yan gudun hijira, da matsalolin tattalin arziki da kuma rashin tsaro.
Game da rikicin Siriya kuwa, Obama ya ce babu wata nasarar da matakin soji sai haifar, sannan ya ce dole a bi hanyar diflomasiyya.