Daya daga cikin wadanda ake zargi da hannu a makarkashiyar neman yiwa jakaden kasar Saudiyya a nan Amurka kisan gilla, ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.
A yau Litinin Manssor Arbabsiar, ya ki amsa laifin a wata kotun birnin New York. Ana tuhumarshi da kokarin neman hanyar wata kungiyar dillalan miyagun kwayoyi ta ‘yan kasar Mexico, ta yi kisan gilla ga jakaden kasar Saudiyya Adel-al-Jubeir ta hanyar tayar da boma-bomai a wani gidan cin abinci a nan Washington DC.
Jami’an gwamnatin Amurka sun yi zargin cewa, Arbabsiar na da hannu a cikin wata makarkashiyar dala miliyan daya da rabi ta neman yin kisan gilla ga jakadan Saudiyya a nan Amurka, wanda rundunar jami’an tsaron juyin juya halin kasar Iran ta shirya. Na biyun da ake zargi Gholam Shakuri, ya yi sa’ar tserewa, amma an yi amanna yana kasar Iran.
Iran ta musanta cewa tana da hannu a cikin wannan al’amarin. Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad ya gayawa tashar talabijin ta CNN jiya Lahadi cewa, “Ba mu taba tunanin yiwa Saudiyya illa ba.”
Manssor Arbabsiar dan shekaru 56, mai fasfon Amurka da na Iran, ya dade a nan Amurka yana sayar da motocin kwance a jihar Texas.