Yariman Saudiya Sultan bin Abdul-Aziz ya rasu sakamakon wani ciwo da ba a bayyana ba. Ya rasu ne yana da sama da shekaru tamanin a duniya.
Kafofin sadarwar kasar Saudiya ne suka sanar da mutuwar shi yau asabar da cewar ya mutu a wata kasa inda yake jinya.
Kafofin sadarwar kasashen turai sun ce ya mutu ne a Amurka inda yake jinya.
Yarima Abdul-Aziz yana daya daga cikin sarakunan da suka yi fice a masarautar wanda ake kyautata zaton shine kan gaba a jerin wadanda zasu gaji sarautar. Yarima Abdul-aziz dai ‘yan uba suke da sarki Abdullah.
Ya yi mulki a shekara ta dubu biyu da goma lokacin da aka yiwa sarkin Abdullah tiyata a birnin NY.
Sarkin da kuma yariman sun yi fama da rashin lafiya a cikin ‘yan shekarun nan.
Yarima Sultan ya yi jinya a Amurka a shekara ta dubu biyu da tara domin wani rashin lafiya da ba a bayyana ba. Kafin zuwanshi jinya an same shi da cutar daji.
Yariman ya rike mukamin ministan tsaro da kuma sufurin jiragen sama tun daga shekara ta dubu da dari tara da sittin da uku. Bisa ga cewar ofishin jakadancin kasar Saudiya a nan Amurka, ya taimaka wajen kafa rundunar soji irin ta zamani masarautar.
Ya taba aiki a matsayin ministan sufuri ya kuma yi gwamnan Riyadh.
Labarai daga kasar Saudiya na nuni da cewa, za a yiwa yarima Sultan jana’iza ranar Talata makon gobe.