Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba a Zaman Dardar a Uganda- 'Yan sanda


Magoya bayan dan takarar shugaban kasa Kizza Besigye
Magoya bayan dan takarar shugaban kasa Kizza Besigye

‘Yan sanda kasar Uganda sun musanta rahotanni da wasu kafafan yada labarai ke bayarwa, na cewa zaman dar-dar din da ake yi a daidai wannan lokaci na yakin neman zaben shugaban kasar, ka iya yin tasiri akan zaben, wanda za a yi a ranar 18 ga watan Fabrairun.

‘Yan sandan sun kara da cewa suna aiki kafada da kafada da sojoji da kuma sauran jami’an tsaro domin ganin an yi zaben ciki kwanciyar hankali.

Wannan batu ya taso ne a daidai lokcin da hukumomin kasar suka haramta yin amfani da mutum-mutumi gabanin zaben.

Hukumar zaben kasar ta ce ta lura akwai karuwar masu amfani da wannan tsari wajen yin kamfen dinsu, duk da cewa ta haramta yin hakan tun a shekarar 2010.

Kakakin ‘Yan sanda, Fred Enanga, ya ce sun kaddamar da wani aikin cire duk wani mutum-mutumi, domin a cewarsa hakan ka iya barzana ga tsaro a lokutan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu da kuma na kananan hukumomi.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG