Barrister Salihu Huseini Garingabas kakakin kwamitin riko na jam'iyyar APC a jihar Jigawa shi ya yi zargin cewa a zaben da aka yi a Hadeija PDO da AC duk jami'an 'yansanda sun kama jami'an zabe da suka yi magudi amma kwamishanan 'yansandan ya bada umurnin a sakesu. Ya ce shi kwamishanan yanzu yana barazanar zai kama Ishaku Hadeija domin an zargi 'yansanda.
Garingabas ya umurci kwamishanan 'yansandan da ya je ya fara gina wurin tsare mutane daga yanzu har shekara 2015 domin shi ne ya kaucewa aikinsa na 'yansanda yana neman ya shigo siyasa. Idan zai iya ya cire kakinsa na 'yansanda ya shiga PDP su kara da shi. Ya kara da cewa hakinsa ne ya kare kowa kowace jam'iyya mutum yake. Babu ruwansa da siyasa. Amma abun da ya keyi a jihar Jigawa ya ishesu.
Amma DSP Abdu Jinjiri kakakin 'yansandan jihar ya ce su basu ce zasu kama Ishaku Hadeija ba. Amma akwai lamun batanci da yayi cewa wai an ga 'yansanda da akwatunan zabe. Ya ce su a garesu kamar cin fuska ne. Su 'yansanda babu ruwansu da akwatunan zabe ko siyasa. Abun da zasu yi shi ne zasu gayyato shi ya zo ya yi masu bayani kan abun da ya gani. Ya nuna masu shaida, wa ya gani, a wane wuri, a wane lokaci. Zasu tabbatar an yi cikakken bincike kan lamarin.
Jami'iyyar PDP ta yi watsi da zargin. Alhaji Salisu Mamuda shugaban PDP a jihar Jigawa ya ce duk wanda ya yi irin wannan maganar bai san abun da ake nufi da doka da oda ba. Hukumar 'yansanda babu abun da ya hadata da gwamnatin Jigawa ko PDP.