Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yansanda da Ali Kwara sun kwato wadanda wasu bata gari ke garkuwa dasu a Adamawa


Solomon Arase babban sifeton 'yansandan Najeriya
Solomon Arase babban sifeton 'yansandan Najeriya

Sace mutane a Najeriya ya zama tamkar ruwan dare gama gari wadda ta samo asli daga kudancin kasar yanzu kuma to soma yaduwa a koina.

Aikin na hadin gwiwa tsakanin Ali Kwara da 'yansanda ya kaiga gagarumar nasara saboda an kwato mutane da kudaden fansa da bata garin suka amsa da makamai a wani yankin jihar Adamawa.

An samu an kashe wasu kasungurmai 'yan fashi da makami da suka addabi wasu sassan jihohin arewacin Najeriya.

An nuna wa manema labarai gawarwakin bata garin da aka kashe tare da bindigogin da aka kwato.

Kakakin rundunar 'yansandan jihar Adamawa DSP Usman Abubakar yace sun samu bankado wasu gungun miyagun mutane masu garkuwa da mutane suna neman kudin fansa. Yace akwai rundunar 'yansanda ta musamman da babban sifetonsu ya kafa wadda ta hada da shi Ali Kwara domin yaki da masu fashi da makami da kuma yin garkuwa da mutane.

DSP Usman yace Allah ya basu nasara domin sun kashe uku cikinsu sauran kuma sun tsere da munanan raunuka. Usman yace sun sami bindigogi guda tara da kudaden Najeriya da na kasashen dake makwaftaka da ita. Sun samu albarusai 477.

DSP Usman Abubakar ya mikawa mutanen kudaden da suka fara biya a matsayin kudin fansa domin a sako masu 'ya'yansu. Su ma sun nuna farin cikinsu da abun da aka yi masu saboda ga 'ya'yansy ga kuma kudadensu. Mutanen sun yabawa 'yansanda da Ali Kwara.

Ali Kwara yace zasu cigaba da aikin domin bata gari sun raba makamai daga Adamawa zuwa Borno, Hadeija da wasu wuraren a arewa.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00

XS
SM
MD
LG