Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Bauchi ta nemi taimakon sojojin sama su zakulo 'yan Boko Haram dake boye cikin dazuka


Sojojin Najeriya a kan babura domin zakulo 'yan Boko Haram
Sojojin Najeriya a kan babura domin zakulo 'yan Boko Haram

A kokarin da take yi gwamnatin jihar Bauchi ta nemi taimakon mayakan sojojin saman Najeriya da su yi anfani da jirginsu na leken asiri su zakulo 'yan Boko Haram da watakila sun fake cikin dazukan jihar.

Banda jihohin Adamawa, Borno da Yobe ita ma jihar Bauchi ta sha fama da hare-haren 'yan Boko Haram da dama.

Akwai labarun cewa 'ayn Boko Haram na fakewa a wasu dazukan jihar lamarin da ya sa kowa na shakkar dorewar zaman lafiya a jihar.

A firar da gwamnan jihar Barrister M. A. Abubakar ya yi da Muryar Amurka ya bayyana abun da jihar ta yi. Yace sun yi wani shirin siri na musamman da ya baiwa sojojin Najeriya damar shiga dazukan.

Makonni biyu da suka gabata gwamna ya nemi taimako na musamman daga sojojin saman Najeriya sun yi anfani da jirgin samansu mai naurar ganin komi dake cikin dazukan. Sun zagaye dazukan kaf basu ga sansanin 'yan ta'adan ba a jihar. Baicin sojojin sama na kasan ma sun shiga dazukan.

To saidai wani masanin aikin sojida harkokin leken asiri ya bana umurni a nemi labarin siri daga wurin jama'a, wato ana binsu ana tambaya.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG