Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mata ‘Yan Kunar Bakin Wake Sunyi Shigar Maza Sun Saje Da Masallata


‘yar kunar bakin waken ta shiga Masallaci da tada bom din dake jikinta.

Wani bom ya tashi da sanyin safiyar yau a wani Masallaci a kauyen Umarari, dake Maiduguri.

Bom din wanda wasu ‘yan kunar bakin wake mata suka tada sunyi shigar maza ne suka saje da masallata, alokacin da daya daga cikin ‘yar kunar bakin waken ta shiga Masallaci da tada bom din dake jikinta.

Ita kuwa ta biyun a karkashin wata bishiya ne ta aikata nata mugun nufin, alokacin data fara ihu tana neman a taimakamata jama’a suka rugo da niyyar kawo dauki sai ta matsa kunamar bom din inda ya hallaka wadanda suka kawo dauki.

Hukumar bada agajin gaggawa na jihar Borno, tace mutane ashirin da hudu ne suka rasu wasu da dama kuma suka samu raunuka, kamar yadda wakilin muryar Amurka Haruna Dauda, ya shaida mana.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG