Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yanbindiga Sun Hallaka Akalla Mutane 4 tare da jikkata Wasu da Dama A Jihar Neja


Yan bindiga
Yan bindiga

Mahara dauke da manyan bindigogi akan babura sun auka a garin Gidigori a karamar Hukumar Rafi inda Bayan sun hallaka mutane sun kuma kona gidaje tare da yin garkuwa da wasu mutanen garin da dama,

Wani Mazaunin Yankin da ya bukaci a sakaya sunanshi ya shaidawa Muryar Amurka cewa, ya zuwa lokacin da suke jana'izar wadanda maharan su ka kashe, mazauna yankin na cikin wani yanayi na tashin hankali.

Rundunar 'yan sanda ta jihar Neja ta tabbatar da kai wannan sabon hari,

A hirar shi da Muryar Amurka, kwamishinan 'yan sanda na jihar Neja Monday Bala kuryas yace su na kan tantance ainihin abinda ya faru. Bisa ga cewar shi, sun tura karin jami'an tsaro a yankin domin farautar maharan da kuma tantance lamarin.

Ya zuwa Lokacin hada wannan rahoto dai babu wani karin haske daga gwamnatin jihar Nejan akan wannan hari na garin Gidigorin,

Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari cikin sauti:

Yanbindiga Sun Hallaka Akalla Mutane 4A Jihar Neja-3:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:16 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG