Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Sama Da ‘Yan Bindiga 200 A Harin Da Jami’an Tsaro Suka Kai Jihar Naija


Wani dan bindiga da jami'ai suka kashe
Wani dan bindiga da jami'ai suka kashe

Akalla ‘yan bindiga 200 ne aka kashe a cikin kwanaki ukun da suka gabata a jihar Niger da ke tsakiyar arewacin Najeriya, a wani samame da jami’an tsaro suka yi na fatattakar ‘yan bindiga daga yankin, kamar yadda kwamishinan jihar ya bayyana a ranar Alhamis.

‘Yan bindiga sun addabi ‘yan kasar a arewaci da arewa maso yammacin kasar inda suka yi kaurin suna wajen sace daruruwan dalibai da mazauna kauyuka domin neman kudin fansa tare da kashe mutane da dama.

Kwamishinan tsaron cikin gida na yankin Neja, Emmanuel Umar, ya ce wasu shugabannin kungiyoyin ‘yan bindiga na daga cikin wadanda aka kashe a wani samame da sojoji suka jagoranta tare da haddin gwiwar ‘yan sa kai na kungiyoyin ‘yan bangan yankin da shugabannin al’umma.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Umar ya ce an kwato babura 60 da ‘yan kungiyar ke amfani don kai farmaki kan kauyuka, da kuma makamai da shanu daga hannun ‘yan bindigar da ke aiki a sansanoni da ke cikin dazuzzukan jihar.

Wani mai magana da yawun rundunar bai amsa tambayoyi nan take da aka masa ba.

Akalla jami’an tsaron Najeriya hudu ne suka mutu lokacin da motar sintirin ta hau kan nakiya a jihar a watan da ya gabata, kuma ‘yan bindiga sun kashe mutane da ba a san adadinsu ba.

Hukumomin yankin Niger sun ce a shekarar da ta gabata, yan bindigan sun kafa sansani a wani yanki a karon farko.

A watan da ya gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce sojoji sun fara wani gagarumin farmaki kan mayakan da ke can.

~ REUTERS

XS
SM
MD
LG