Yayin da 'yan kasar Zimbabwe suka dunguma zuwa rumfunan zabe domin kada kuri'unsu a zaben shugaban kasar, tsohon shugaba Robert Mugabe ya soki jam'iyar ZANU-PF mai mulki.
"Ba zan zabi mutanen da suka kuntata mini ba," Mugabe ya fadawa manema labarai da ya gayyata zuwa gidansa da ke wata unguwar masu hali a Harare.
Da aka tambaye shi wanda ya zai jefawa kuri'a Mugabe yaki ya ba da amsa.
Wannan shi ne zabe na farko cikin shekaru 38, da Mugabe ba ya takara a matsayin shugaban jam'iyyar ZANU-PF.
Mugabe dan shekaru 94 da haifuwa, ya yi murabus cikin watan Nuwamban bara, sakamakon matsin lamba daga sojojin kasar.
Mutumin da ya dade yana mataimakinsa, dan shekaru 75 da haifuwa Emmerson Mnangagwa,shi ne ya gaji Mugabe, kuma yake takara na shugabancin kasar a yau.
Ko da yake, mutane 23 ne suka yi rijistar za su yi takarar shugabancin kasar, daga karshe dai ana kallon takarar tsakanin mutane biyu ne - Mnangagwa-wanda yake fuskanatar kalubale mai tsanani daga sabon shugaban babbar jam'iyyar hamayya, dan shekaru 40 da haifuwa Nelson Chamisa.
Mugabe ya bayyana fatar zaben zai bude sabon babi a Zimbabwe, fatar da sauran 'yan takara su ma ma suke yi.
Facebook Forum