Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Somalia da Eritrea Na Shirin Sake Bude Ofisoshin Jakandancin Su A Kasashesn


Daga hagu, Shugaban Eritrea Isaias Afwerki, da bakonsa Shugaba Mohamed Abdullahi Farmajo na Somalia
Daga hagu, Shugaban Eritrea Isaias Afwerki, da bakonsa Shugaba Mohamed Abdullahi Farmajo na Somalia

Shugabannin Somalia da Eritrea sun amince a yau Lahadi su dawo da huldarsu ta diplomaisya kana su bude ofisoshin jakadanci a kasashen juna.

An yanke wannan shawara ce a wani taron koli a birnin Asmara na kasar Eritrea, inda shugaban Somalia Mohamed Abdullahi Farmajo ya fara wata zaiyarar kwanki uku mai cike da tarihi a yau Lahadi. Huldar kasashen ta yanke ne kusan shekaru goma sha biyar.

Da yake zantawa da sashen Somaliyanci na Muryar Amurka, ministan yada labarai na Somalia Dahir Mohamed Geelle, yace nan bada dadewa ba zaku ga jakadun Eritrea da Somalia a manyan biranen kasashen biyu.

Yace shugabannin biyu sun tattauna a kan makomar tsaron yankin da kuma musayar alaka tsakanin kasashen Afrika dake kan gabar tekun bahar maliya.

Shugabannin zasu ci gaba da tattauanawarsu a yau Lahadi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG