Jiya litinin ‘yan kasar Zimbabwe suka jefa kuri'a wanda ke cike da tasiri ga kasar, wanda kuma suke sa ran ya sauya tattalin arzikinsu da ya sukurkuce da martabar kasar da ta zube a fuskar duniya a karkashin tsohon shugaban kasar Robert Mugabe wanda ya kwashe shekaru 38 yana musu mulkin kama karya.
Masu sa ido a zaben cikin birnin Harare fadar Gwamnatin kasar basu bada bayanin wani tashin tashina ba har zuwa lokacin da za a rufe runfunar zaben da yammaci.
Elmar Brock shugaban tawagar tarayyar Turai da na masu sa ido a zaben, yace a wasu sassan kasar, zaben ya tafi kan tsari amma a wasu sassan ko an yi zaben sai dai babu tsari sam.
Facebook Forum