Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Kama Dan Kasar Iran Kan Zargin Ta'addanci a Brazil


Wasu 'Yan Sandan Brazil
Wasu 'Yan Sandan Brazil

‘Yan sanda a Brazil sun cafke wani dan kasar Iran, bisa zargin alaka da ta’addanci a birnin Chui a yankin Kudancin kasarsu.

Jami’an leken asiri sun dade suna bin sawun al’amuransa tun daga 15 ga Yulin da ya wuce. Tuni aka gabatarwa da Pouria Paykani takardar amincewa da kama shi da kuma takardun da ke nuna an yarda da a maida shi kasarsu.

An kuma kama shine a yana kokarin shiga Uruguay a motar haya ta Bas. Ma’aikatar gwamnatin tarayyar kasar akan lamuran jama’a tace, an mika takardun fitar da shi daga kasar ne sakamakon zaman cikinta ba bisa ka'ida ba.

Sun bayyana cewa, wannan ka’idar doka ta yin waje rod da mutum, itace ka’idar kasar akan duk wani mutumin da ya shiga kasar ta Brazil ba tare da ka’ida ba, ko yake zaune ba da izini ba.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG