Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obama Ya Yiwa 'Yan Wasan Amurka Fatan Nasara a Wasan Olympic


Shugaban Amurka, Barack Obama
Shugaban Amurka, Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama, ya yi fatan Alheri da nasara ga ‘yan wasan Amurka TEAM USA, da ke halartar wasannin Olympic da aka fara a jiya a birnin Rio na kasar Brazil.

Inda ya kara godewa ‘yan wasan kasar har ma da ‘yan wasan nakasassu bisa kwazonsu. Ya bayyana cewa yan wasan suna wakiltar katafariyar kasar Amurka mai albarka.

Kasar da ke bada daga ga ‘ya’yanta ba tare nuna wariyar akan asalin inda suka fito ba. Matukar mutum na da tarbiyya da hangen mnesa da kuma kishin kasar.

Wannan wasan Olimpiya shine na farko da wata kasar Kudancin Amurka ta karbiu bakuncinsa. Ya kara dac cewa, ‘yan wasanni daban daban na Amurkar sun fito ne daga jihohi 46.

Sai kuma babban birnin tarayya wato nan Washington da kuma yankin tsibirin da ake cewa Virgin Islands. Karshe shugaban ya rufe da cewa, su je su kwaso gwala-gwalen lambobin yabo.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG