Tsohon shugaban kasar Yamal Ali Abdullah Saleh ya ce a shirye yake ya tattauna da rundunar gamayyar da Saudiyya ke jagoranta wacce ke marawa gwamnati baya.
Saleh yayi wannan magana ne a dai-dai lokacin da ‘yan tawaye dake goyon bayansa ke ci gaba da fada da rundunar hadin gwiwar a babban birnin Sana’a.
Amma wannan tayi yazo da sharadi, Saleh ya ce zai shiga tattaunawar ne idan har Saudiyya ta kawo karshen hana shigo da kaya kasar.
Da yake magana da gidan talabijin Saleh ya ce “Ina kira ga ‘yan uwanmu dake makwabtan kasashe….Da dakatar da hare-haren da suka kai mana su kuma kawo karshen rufe iyakokinmu.
A halin yanzu dai ana ci gaba da fada. Kafar yada labarai ta AP ta rawaito wasu mazauna birnin na cewa sun ji karar fashewa masu karfin gaske a daren Jum’a da safiyar jiya Asabar a birnin Sana’a.
Sai dai babu wani bayani kan yawan mutanen da fadan na baya-bayan nan ya rutsa da su.
Facebook Forum