Makaman da ‘yan tawayen suka mikawa hukumomi sun hada da manya da kananan makamai da kuma alburusai
'Yan tawayen sun ajiye makamansu yayin wani biki da aka gudanar karakashin jagorancin gwamnan jihar Agadas Birgediya Janar Ibrah Issa Bulama.
Ta hanyar wani kwamiti ne dake shiga tsakani wanda gwamnatin mulkin sojojin Nijar ta kafa mai mambobi 17 da ta daurawa alhakin shawo kan ‘yan tawayen domin rungumar zaman lafiya, kwamitin ya yi nasarar wayar da kan wadannan ‘yan tawayen da suka ajiye makamansu, da kuma muhimmancin da zaman lafiya ke da shi a cikin kasa.
A kwanakin da suka gabata ne wasu manyan jiga-jigen kungiyoyin tawayen, ciki har da kakakin kungiyar tare da wasu kwamandoji uku suka bar fafutukar, tare da cewa sun yanke shawarar zaman lafiya.
To sai dai kungiyoyin fafutuka na ganin dole ne gwamnatin Nijar ta yi taka tsantsan da kuma sanya ido sosai a kan tsofaffin ‘yan tawayen domin gudun kar a koma gidan jiya inji Abdourahmane Bianou wani ‘dan fafutuka a Agadas.
Wannan sabon mataki na mika wuya da ‘yan tawayen ke yi da kuma rungumar zaman lafiya ya kawo sabon fata da gwamnatin Nijar ke yi na inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin kasar.
Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud:
Dandalin Mu Tattauna