Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Diffa: ‘Yan Boko Haram Na Ci Gaba Da Tuba


Wasu Mayakan ISWAP Da Boko Haram Da Iyalansu Da Suka Mika Wuya
Wasu Mayakan ISWAP Da Boko Haram Da Iyalansu Da Suka Mika Wuya

A ci gaba da nasara da ake yi kan mayakan Boko Haram a kasashen Najeriya, Chadi, Kamaru, da Nijar, an sake samun wasu daga cikin 'yan bindigar da su ka mika wuya a yankin Diffa na Jamhuriyar Nijar

‘Yan Boko Haram na ci gaba da tuba a jahar Diffa da ke gabashin Jamhuriyar Nijar da ma sauran wuraren na gabashi, inda a yanzu haka mahukunta ke cigaba da karbar tubabbun mayakan Boko haram din waddanda suka mika wuya bisa radin kansu, a wani mataki na sake saka su a cikin al'umma amma bayan haras da su ta hanyar sauya musu tunani zuwa mai kau.

Yanzu an sake samun ‘yan Boko Haram sama da 700 da su ka tuba. Waddannan tubabbun dai a halin yanzu na gudanar mu'amalar zamantakewarsu tsakaninsu da al'umma, inda sannu a hankali su ke sabawa da rayuwar yau da kullum baya ga horas da su din da za a yin a musamman.

Jihar ta Diffa, wadda ke makwabtaka da Najeriya fa Chadi, ta yi fama da hare haren Boko Haram a shekarun da su ka gabata, al’amarin da ya yi sanadin mace macen mutane da dama ciki har da yara kanana da mata. Wannan ya sa da dama daga cikin ‘yan yankin sun gudu zuwa wasu sassan kasar, baya ga wadanda su ka ketara zuwa wasu kasashe makwabta.

Idan an tuna dai, a jahar ta Diffa tun a shekara ta 2015 aka fara rikicin Boko Haram, lokacin da har ta kai ga hukumomin yankin na ta kokarin yin yarjejeniyoyin sulhu da ‘yan Boko Haram. Bayan da aka fara cimma jituwa, sai ‘yan bindigar Boko Haram din su ka fara mika wuya a 2016, inda nan take aka shiga tura su a wata cibiyar da ke sake daidaita hankalinsu da Gudumariya, jahar ta Diffa.

A shekara ta 2019 kuwa mahukuntan jahar Diffa na lokacin su ka umurci fara tura tubabbun zuwa ga ‘yan uwansu.

Malam Kyari Ari, daya daga cikin tubabbun farko da su ka aje makamansu a jahar Diffa, kuma kawo yanzu su ke zaman lafiya da jama’a, ya bayyana cewa an yaudare su ne su ka shiga Bako Haram. Ya yi kira ga hukumomi da su taimaka ma su da abin yin sana’a don samun abin zaman gari.

Su ma mutanen gari sun bayar da kyakkyawar shaida kan tubabban ‘yan Boko Haram din da cewa su na cikakken zaman lafiya da su.

A saurari cikakken rahoton Haru Sulai Rasheedu:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG