Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kasar Ghana Sun Caccaki Frayim Ministan Birtaniya Da Kakkausan Lafazi


Frayim Ministan kasar Birtaniya David Cameron. (file photo)
Frayim Ministan kasar Birtaniya David Cameron. (file photo)

Barazanar katse taimakon da David Cameron ya yiwa Ghana ta hasala 'yan kasar

Kamar yadda wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka a Accra Baba Yakubu Makeri ya aiko ma na Frayim Ministan kasar Birtaniya ya yiwa wasu kasashen Afirka barazanar janye taimakon kudaden da Birtaniya ke ba su a kowace shekara idan ba su baiwa 'yan madigo da 'yan luwadi 'yanci ba. A cikin kasashen har da kasar Ghana.

Kasar Birtaniya ta na tallafawa kasafin kudin kasar Ghana a kowace shekara kuma Frayim Minista David Cameron yayi wannan barazana ce a daidai lokacin da Birtaniya ta yi alkawarin karawa Ghanar fam miliyan 370 a cikin kasafin kudinta na bana.

Sauri:

Bayan Barazanar ta Frayim Ministan Birtaniya David Cameron 'yan kasar Ghana masu dimbin yawa sun maida martani da kakkausan lafazi, kuma bakin su ya zo kusan daya cewa Birtaniyar ta janye taimakon nata, kuma Allah ne mai taimako ba mutum ba, su ka ce addinan Musulunci da na Kirista ba su yarda da mummunar tabi'ar madigo da luwadi ba.

Sarkin Fadama alhaji Rilwanu Abbas shi ma yayi tur da Allah waddai da wannan barazana ta kasar Birtaniya inda ya ce wannan magana ba ta ma taso ba domin ko da wasa ba abun da 'yan kasar Ghana za su amince da shi ba ne. Ya ce addinin Musulunci ya haramta madigo da luwadi da ma duk wani abu dangin zina gaba daya. Alhaji Rilwanu Abbas ya ce gara yunwa ta kashe 'yan kasar Ghana da a ce sun bada kai bori ya hau game da wannan batu. Ya ce wannan cin fuska ne ma da kuma raini, sannan ya bayyana takaicin shi na ganin yadda kasashen Afirka ke ci gaba da dogara akan Turawa duk da dimbin arzikin da Allah Ya yi musu.Ya ce mutuwar zuciya da lalaci da sakaci sune suka kai kasashen Afirka ga dogara kan wasu kasashen da su ne ya kamata su dogara a kan su, kuma wannan ya nuna cewa har yanzu kasashen Afirka na karkashin mulkin mallaka.

Duka addinan kasar Ghana har da na gargajiya sun yi Allah waddai da wannan abu sannan suka ce wannan zai iya kawo cikas ga kokarin da ake yi na yakar luwadi da madigo a kasar Ghana.

Alhaji Huseini Maiga jigo a jam'iyyar hamayyar kasar Ghana ta NPP, ya ce akwai bukatar 'yan kasar Ghana su yi watsi da wannan maganar gwamnatin kasar Birtaniya su hada karfi su yaki wannan abu tare.

Har yanzu dai gwamnatin kasar Ghana ba ta bayyana matsayin ta akan wannan magana ba.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG