Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Ta'adda Sun Kama Wasu Kauyukan Yankin Zuru A Jihar Kebbi


Gwamnan Kebbi Abubakar Atiku Bagudu.
Gwamnan Kebbi Abubakar Atiku Bagudu.

À Najeriya tabarbarewar rashin tsaro har ya kai ga ‘yan ta’adda ke da iko da wasu kauyuka a wasu sassa na arewacin kasar.

Yankin Zuru na daga cikin wuraren da ‘yan ta’adda ke rike da wasu kauyuka saboda sun addabi jama’ar kauyukan har sun yi kaura sun bar musu wuraren; wadanda suka rage kuma suna karkashin ikon ‘yan ta’addan.

‘Yan Najeriya dai sun dade suna kokawa a kan yadda rashin tsaro ke ci gaba da tabarbarewa, yayin da su kuma hukumomi ke cewa suna daukar matakai don magance matsalolin.

Karin bayani akan: DSP Nafi’u Abubakar, Operation Ganuwa, jihar Zamfara, jihar Kebbi​, Nigeria, da Najeriya.

Yankin Zuru a jihar Kebbi na daga cikin wuraren da matsalar ko ta yi sauki sai kuma ta dawo, abin har ya kai ga ‘yan bindiga sun mamaye wasu kauyuka.

Salihu Muhammad Bena, mazaunin Bena ne ta karamar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi​. Ya ce ‘yan ta’addan suna rike da kauyuka da ke kan iyaka da jihar Zamfara​, don haka ne mazauna kauyukan su ka arce zuwa garin Bena domin samun mafaka.”

Buhari Riba shi ma mazaunin yankin ne da ke fama da matsalar ‘yan bindiga. Ya ce an kawo musu jami’an tsaro amma kuma ba su da isassun kayan aikin farautar ‘yan bindigar.

Shi ma shugaban kungiyar ‘yan sa kai na yankin ya tabbatar da cewa lallai ‘yan bindiga su ne suka mamaye mafi yawan garuruwan da ke makwabtaka da yankin Zuru daga jihar Zamfara.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar ta ce ta kaddamar da shirin "Operation Ganuwa” wanda ke da zummar zagaye jihar da jami’an tsaro ta yadda ‘yan ta’adda daga wasu jihohi ba za su samu sukunin kutso kai cikin jihar ba har su yi barna.

Wakilin Muryar Amurka ya tuntubi rundunar don jin halin da ake ciki a kan wannan batun, kakakin rundunar DSP Nafi’u Abubakar ya ce ana kan gudanar da shirin kuma yana tasiri.

Dangane da rashin isassun ababen hawa ga jami’an kuwa ya ce jama’a su dan kara hakuri.

Masu lura da al’amurra dai na ganin akwai bukatar hukumomi su yi da gaske domin shawo kan matsalolin rashin tsaron domin ba a san yadda lamarin zai kaya ba idan aka yi sako sako da shi.

Ga rahoton Muhammad Nasir daga Sokoto:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG