Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Siyasa A Jihar Zamfara Na Ci Gaba Da Caccakar Matakan Da Gwamnatin Tarayya Ta Dauka A Jihar


Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle.
Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle.

Jami'an gwamnatin jihar Zamfara da 'yan siyasa, sun ci gaba da sukar lamirin gwamnatin tarayyar Najeriya, na haramta zirga-zirgar jiragen sama a jihar Zamfara, da kuma dakatar da ayukan hakar zinari a jihar, a zaman wasu daga cikin hanyoyin dakile ayukan ta'addanci a jihar.

Na baya-bayan na shi ne shugaban jam'iyyar APGA a jihar ta Zamfara Dr. Sani Abdullahi Shinkafi, wanda kuma babban makusanci ne ga gwamnan jihar, Bello Mohammed Matawalle.

Shinkafi wanda kuma shi ne babban daraktan kungiyar rajin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban al’umma, ya ce ikirarin cewa jirage masu saukar ungulu na bayar da makamai domin sayen zinarin da ake hakowa a jihar ta Zamfara, cin fuska ne ga hukumomin tsaron Najeriya.

Karin bayani akan: Zamfara, Bello Matawalle, APGA, Nigeria, da Najeriya.

A cikin wata sanarwa da ya rattabawa hannu, Shinkafi ya ce wannan ikrarin ya nuna gazawa a bangaren hukumomin tsaron kasar da nauyin tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma ya rataya a kan su, ya na mai cewa, lamarin ya bayyana wa duniya gazawar hukumar kula da harkokin sufurin jiragen sama ta NAMA.

Nauyi ne kan hukumar kula da harkokin sufurin jiragen sama na NAMA ta sa ido tare da baiwa jirage masu shawagi a sararin samaiyar Najeriya lasisi kafun keta hazo amma hukumar ta gwamnati ta gaza, don haka ga duk wanda zai ce jirage sun shigo jihar ta Zamfara don sauke makamai su karma gwal ba tare da hadin kan hukumar NAMA da ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ba, yana boye gaskiyar lamarin, in ji Shinkafi.

XS
SM
MD
LG