Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Alaka Tsakanin Hakar Ma’adanai Da Ayukan Ta’addanci A Jihar Zamfara – Matawalle


Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle.
Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle.

Gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle ya ce ayukan ta’addanci da ‘yan bindiga ke yi a jihar ba su da alaka da hakar ma’adanai musamman zinari da ake yi a wasu sassan jihar.

Matawalle yana mai da martani ne akan dokokin da gwamnatin tarayya ta kakaba a jihar, da zimmar yaki da ta’addanci a jihar.

Jim kadan bayan da aka sako daliban makarantar sakandaren mata ta Jangebe su 279 da ‘yan bindiga suka yi awon gaba da su a wani farmaki da suka kai a makarantar, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ayyana wasu dokoki a jihar ta Zamfara, da suka hada da haramta shawagin jiragen sama, da umarnin kashe duk wanda aka gani da bindigar AK-47 ba bisa ka’ida ba da kuma haramta hakar ma’adanai a jihar.

Karin bayani akan: Zamfara, Bello Matawalle, AK-47, Nigeria, da Najeriya.

To sai dai yayin da yake marhabin da sababbin manyan hafsoshin tsaron Najeriya da suka kai ziyarar aiki a Gusau, fadar gwamnatin jihar a karkashin babban hafsan tsaro, Gwamna Matawalle ya ce akwai ayukan hakan zinari da ake yi a wurare da dama na jihar da hukuma ta amince da su, kuma yanzu haka jami’an gwamnatin tarayya na sanya ido akan yadda ake hako ma’adanin a jihar.

Gwamnan jihar Zamfara tare da manyan hafsoshin tsaron Najeriya
Gwamnan jihar Zamfara tare da manyan hafsoshin tsaron Najeriya

Ya kara da cewa su kan su masu hakan ma’adinan ma ba su tsira ba, domin kuwa sau tari ‘yan bindigar na kai musu hari, suna kuma sace wasu daga cikin su, wanda hakan ke nuna basu da alaka da ‘yan ta’addar.

To sai dai duk da haka ya yabawa gwamnatin tarayya akan kafa dokokin, wadanda ya ce hakika za su taimaka wajen kawo karshen ta da kayar baya a jihar, da ma sauran jihohin da ke fama da kalubalen tsaro.

Haka kuma gwamnan ya godewa shugaban kasa akan amincewa da shirin sulhu da yake yi, wanda ya ce ya soma tasiri a jihar.

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle
Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle

Tun da farko dai Sarkin Zamfaran Anka, kuma shugaban majalisar sarakuna ta jihar Alhaji Attahiru Ahmad ne ya soma bijiro da zancen dokar ta dakatar da ayukan hako ma’adinai a jihar, inda ya ce ya kamata a yi la’akari da dimbin jama’a musamman matasa da ke neman abinci ta wannan hanyar.

“Da ma ana ganin matsalar rashin aikin yi na daga cikin abubuwan da suke kara uzzura kalubalen tsaro. Don haka muna fargabar makomar matasan da ke wannan sana’a ta hako ma’adinai idan suka rasa aikin na su”, in ji Mai martaba Sarkin Zamfaran Anka.

Gwamnan Jihar Zamfara yana ganawa da manyan hafsoshin tsaron Najeriya a Gusau
Gwamnan Jihar Zamfara yana ganawa da manyan hafsoshin tsaron Najeriya a Gusau

Bayan gudanar da wani taro a kebance tare da manyan hafsoshin tsaron, Gwamnan na Zamfara Bello Matawalle, shi kuma ya ayyana wasu sababbin dokoki da gwamnatin jihar ta kafa, domin marawa kokarin gwamnatin tarayya na samar da tsaro.

Dokokin sun hada da wa’adin wata biyu ga dukan ‘yan bindigar da ba su ajiye makamansu ba da su zo su ba da kai, haramta hawan babur fiye da mutum biyu, da kuma jerin gwanon Babura suna tafiya a lokaci daya.

Haka kuma gwamnatin jihar ta umarci dukkan jami’anta da sarakunan gargajiya da su kasance a yankunasu na asali akai-akai, ta yadda za su rika sanya ido akan lamurran ke faruwa, a yayin da kuma aka gargadi ‘yan sa kai a jihar da su mutunta matakin gwamnati na dakatar da ayukansu, ko su fuskanci dokar rika makami ta shugaban kasa.

Ga Gwamna Matawalle yana bayyana sababbin dokokin da gwamnatin jihar ta Zamfara ta kafa:

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Mohammed Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

Babban Hafsan Hafsoshin tsaro Major-General Lucky E.O Irabor, yana tare ne da rakiyar babban hafsan sojan kasa Major-General Ibrahim Attahiru, da na sojan ruwa Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo da kuma na sojin sama Air-Vice Marshal Ishiaka Oladayo Amao.

Major-General Lucky E.O Irabor ya ce sun je jihar ta Zamfara ne domin saduwa da dakarunsu, tare da zimmar karfafa musu gwiwa, da kuma duba yadda za’a kara kaimin yaki da ta’addanci a yankin.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG