Mabiya mazahabr Shi'a a Najeriya sun yi kira ga hukumar zaben kasar, wato,INEC da ta soke rajistar jam'iyyar APC mai mulki.
Reshen kungiyar na jihar Filato ne ya yi wannan kira bisa dalilin cewa gwamnatin APC ta ki bin umurnin kotu, wacce ta yanke hukuncin a saki El-Zakzaky.
Daya daga cikin almajiran Sheikh El-Zakzaky Nura Waziri a Jos a wani taron manema labarai ya bayyana cewa sun rubutawa hukumar zabe akan bukatarsu idan kuma ba ta dauki mataki ba za su garzaya kotu.
A cewarsa, tun a watan Disamban bara kotu ta ba da umurnin a saki shugabansu a kuma biya shi diyya, sannan a mayar masa da gidansa kana a bashi tsaro.
Amma duk hakan ya cutura a cewar Waziri.
Sai dai a martanin da ya mayar, mataimakin shugaban jam'iyyar APC na yankin arewa ta tsakiya, Alhaji Zakari Abdullahi Idi, ya ce an yi rajistan APC a karkashin doka ne idan kuma ta sabawa dokar ba mabiya Shi'a ne za su ce a janye rajistarta ba.
Wannan hurumi ne na hukumar zabe INEC inji Idi.
Saurari rahoton Zainab Babaji domin karin bayani:
Facebook Forum