Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Gangamin Yaki Da Dabi'ar Yi Wa Mata Kaciya A Abuja


'Yan raji, masana da kwararru tare da shugabannin al'umma sun gudanar da wani gangami a Abuja domin yaki da al'adar yi wa mata kaciya, musamman a ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin fadakarwa kan wannan mummunar dabi'a.

Wakilin sashen Hausa a Abuja, Saleh Shehu Ashaka, yace an gudanar da wannan gangami musamman domin fadakar da ungozoma irin matakan da zasu dauka na gano mai fama da wani ciwo dake da alaka da irin wannan kaciya ta mata domin garzayawa da su asibiti maimakon barinsu su haihu a gida a lokacin nakuda.

Wata jami'a mai kula da daidaito a tsakanin jinsuna, Ms. Comfort Mahdi, ta ce mata da yawa da aka yi ma kaciya ba su iya sakewa da miji ko da a gidajensu na aure, abinda ke janyo matsalar zamantakewa, yayin da wasu da yawa daga cikinsu ke fuskantar wahala a lokutan haihuwa.

Ta ce wannan al'ada da ake yi a wasu sassa da nufin hana mata bin maza, babu abinda take haifarwa illa wahala har ma da mutuwa.

Dr. Rilwan Mohammed yace a saboda ganin yadda ake samun karuwar mata masu fama da illolin da suka jibinci kaciyar da aka yi musu, ya sa ala tilas a gudanar da irin wannan fadakarwa a yankunan karkara, inda aka fi yin wannan abu.

Dr. Usman Sa'idu Adamu, yace su na tura jami'ai domin kula da duk wadda aka samu labarin tana fama da wannan matsala.

Ga cikakken rahoton Sale Shehu Ashaka...

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG