Hukumar kula da albarkatun man fetur ta Najeriya, DPR, ta rufe wasu gidajen mai guda a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, a saboda samunsu da ta yi suna aikata wasu abubuwan da suka saba ma doka tare da cutar jama'a.
Shugaban hukiumar ta DPR mai kula da shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, Alhaji Ali Jokana, shine ya dauki wannan matakin rufe gidajen man a lokacin da ya jagoranci 'yan jarida wajen zagayawa domin ganin yadda gidajen mai ke gudanar da ayyukansu a Maiduguri.
Ya ja kunnen dukkan masu gidajen mai da su kawo karshen irin zambatar da suke yi ma jama'a, ko kuma su saka kafar wando guda da wannan hukuma.
Wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda Biu, wanda ya zagaya tare da shugaban hukumar na shiyyar arewa maso gabas, yace gidajen man da aka rufe din an same su ne da laifuffuka da suka kama daga wadanda suke boye mai, da masu tauye lita domin cutar masu sayen mai, da wadanda suke kara farashin man ba tare da izni ba.
Wakilin namu yace a maimakon sayar da man a kan Naira 145 kowace lita, wasu daga cikin wadannan gidajen man su na sayarwa a kan kudi fiye da Naira 200.
Wasu daga cikin masu gidajen man sun yi ikirarin cewa su na sayen man da tsada ne, kuma dole su sayar ta yadda ba zasu fadi ba. Amma shugaban hukumar ta DPR ya musanta wannan, yana mai fadin cewa kowane gidan mai yana da takardun da suka ba shi ikon zuwa Daffo domin saro mai a kan kudin da gwamnati ta kayyade.
An dai shafe wata da watanni ana fama da karancin man da wasu ke dora alhakinsa a kan hukuma, wasu kuma su na cewa dillalai da masu gidajen mai ne ke haddasa karancinsa da gangan domin cutar jama'a.
Ga cikakken rahoton Haruna...
Facebook Forum