‘Yan sandan Misira sun yi arangama da masu zanga-zanga a wadansu birane biyu na gabashin kasar, a kwana ta uku da fara gangamin kin jinin gwamnati a fadin kasar. ‘Yan sanda sun yi ta harba barkonon tsohuwa da albarusan roba a kan masu zanga-zanga a Suez, a yau Alhamis. Masu zanga-zanga a birnin sun banka wa wani ginin gwamnati da ofishin ‘yan sanda wuta jiya da wajen almuru. Wadansu kuma sun yi yinkurin kona hedkwatar jam’iyyar National Democratic Party, kafin ‘yan sanda su fatattake su da barkonon tsohuwa. An ji wa akalla mutane hamsin da biyar rauni a wannan tashin hankalin. Haka kuma, daruruwan masu zanga-zanga sun gwabza da ‘yan sanda a birnin Ismaila. A halin da ake ciki kuma wani fitaccen dan gwagwarmayar canji a Misira na shirin komawa ksar. Mohammed El-Baradei, tsohon Shugaban Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya, ya tashi daga Australiya zuwa al-Khahira a yau domin shiga sahun masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Hosni Mubarak da ya shafe shekaru 30 bisa karagar mulki.