Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu zanga zanga sun yi watsi da dokar hana yawon dare a kasar Misira


Sojojin kasar Misira suna taye kan motocin yaki.a birnin Alkahira, 29 Jan 2011.
Sojojin kasar Misira suna taye kan motocin yaki.a birnin Alkahira, 29 Jan 2011.

Dubu dubatan masu zanga zanga sun yi watsi da dokar hana yawon dare da aka ayyana

Dubu dubatan masu zanga zanga sun yi watsi da dokar hana yawon dare da aka ayyana, suka ci gaba da mamaye titunan birnin Alkahira da sauran biranen kasar Misira yau asabar, suna kira ga shugaban kasar Hosni Mubarak ya yi murabus. Gwamnati ta sanar da dokar hana yawo kama daga karfe hudu agogon yamma na kasar, sa’oi biyu kafin lokacin hana yawon da aka sanar jiya jumm’a, sai dai hotunan da ake yayatawa a tashoshin talabijin yau da yamma suna nuna mutane suna kara tururuwa zuwa babban birnin kasar. Yau aka shiga rana ga biyar ta zanga zanga a duk fadin Misira inda ake neman ganin bayan mulkin shugaba Mubarak da ya shafe shekaru talatin bisa karagar mulki. An baza sojoji a ko’ina cikin gari sai dai babu rahoton da ya nuna cewa suna hana mutanen zanga zanga. Duk da haka, kafofin watsa labarai sun ce an kashe akalla mutum daya lokacin da ‘yan sanda suka bude wuta kan masu zanga zanga kusa da ma’aikatar harkokin cikin gida. Tashar talabijin ta Al Jazeera ta nuna masu zanga zanga suna dauke da gawar wani mutum.Jami’an kasar Misira sun ce mutane talatin da biyar aka kashe a zanga angar ta kwana biyar da suka hada da ‘yan sanda goma, yayinda wadansu kafofin sadarwa suka ce adadin wadanda suka rasu ya haura haka, bisa ga cewarsu, mutane saba'in da hudu aka kashe a zanga zangar da aka yi a manyan birane.

XS
SM
MD
LG