Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Yankin Korea


Shugaban kasar Koriya ta Kudu Lee Myung-bak yana jawabi ga kasa (file photo)
Shugaban kasar Koriya ta Kudu Lee Myung-bak yana jawabi ga kasa (file photo)

Wani babban jami’in Jakadancin Kasar China, ya shaidawa shugaba Lee Myung-bak na Korea ta kudu cewar China zata ci gaba dakokarta ganin an kai ga rage zaman tankiya tsakanin Korea ta Kudu da Korea ta Arewa.

Kamfanin dillancin labarun China,Xinhua ya bada labarin cewa babban jami’in jakadancin kasar China Dai Bingguo, ya shaidawa shugaba Lee Myung-bak na Korea ta kudu cewa China zata ci gaba da kokarin daukan matakan rage zaman dar-dar da ake yi ta hanyar shirya tattaunawa a tsakanin Korea ta kudu da Korea ta Arewa. Jakadan na kasar China ya furta hakan ne a ziyarar day a kai Seoul, babban birnin kasar Korea ta kudu a dai dai lokacin da ake shirin hadin gwiwar rawar dajin rundunar sojin ruwan Amirka da ta Korea ta Kudu.A dai dai lokacin da China ke kokarin shirya sulhu tsakanin Korea ta Kudu da Korea ta Arewa, jami’an Gwamnatin Korea ta Kudu sun bada rahoton cewa anji karar harbe-harben makamai masu linzami daga shiyyar Korea ta Arewa dake yiwa tsibirin kan iyakar Korea ta kudu barazana.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG