An ayyana dokar hana yawon dare a birnin Alkahira na kasar Misira da kuma sauran birane sai dai dokar bata iya shawo kan zanga zangar da dubban mutane suke yi na neman shugaban kasar, Hosni Mubarak ya sauka daga karagar mulki ba. Hotunan bidiyo daga Alkahira na nuna masu zanga zanga suna tura wata motar sojoji da ba kowa a ciki, suna kokarin turata kan gada zuwa cikin tekun Nilu, daga baya suka cinna mata wuta. Ana ganin wuta na ci a wurare da dama na birnin da suka hada da gine ginen gwamnati yayinda ake kuma jin karar bindiga a tituna. Shelkwatar jam’iyar National Democratic mai mulki na daga cikin gine ginen da aka kona. Ayarin motoci dauke da dakaru na ta tururuwa zuwa cikin birnin Alkahira, yayinda Sojoji suke ci gaba da sintiri a Suez inda ‘yan sanda suka yi amfani da barkonon tsohuwa da mesar ruwa da kuma kulake wajen tarwatsa masu zanga zanga. An sami rahoton mutuwar a kalla mutum guda. Ana kyautata zaton nan ba da dewa ba, shugaba Hosni Mubarak zai yi jawabi ga kasa da za a yayata kai tsaye a tashar talabijin yau Jumma’a, ranar da zanga zangar kin jinin gwamnati da aka fara ranar Talata ta fi zafi. Ba a ji daga shugaban kasar dan shekara 82 ba tun da aka fara zanga zagar. Kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya laburta cewa, an yiwa wanda ya sami lambar yabo ta Nobel, Mohammed ElBaradei daurin talala.
An ayyana dokar hana yawon dare a birnin Alkahira na kasar Misira da kuma sauran birane da ke kewaye
Kasar Misira ta ayyana dokar hana yawon dare yayinda zanga zanga ke kara bazuwa.