Jirgin ya fado ne tare da hallaka mutanen guda bakwai ciki har da jakadun kasar Philippines da Norway a Pakistan da kuma matan jakadun kasar Maleysia da Indonesia hade da ma’aikatan jirgin guda uku.
Hukumomi sun fadi cewa gawarwakin mutanen a yanzu haka suna barikin sojojin sama na Nur Khan a garin Rawalpindi. Jami’ai sun ce jirgin yana dauke da a kalla mutane goma sha bakwai a lokacin da ya fadi a ranar juma’a a tsaunin Naltar a arewacin Pakistan.
Kakakin sojojin kasar Manjo Janar Asim Bajwal ya fada a shafinsa na Twitter cewa jakadun kasar Poland da na Netherlands suna cikin wadanda suka sami tsira a hadarin jingin saman.
‘Yan kungiyar Taliban dai sun ce sune da alhakin kakkabo jirgin mai saukar ungulun da niyyar auna samun Firaministan kasar Nawaz Sharif.
Sai dai Ministan Tsaron kasar ta Pakistan Kawaj Asif yace hatsarin ya faru ne sakamakon matsalar na’ura ba wai saboda harin ‘yan ta’adda ba.