Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Jamus Sun Kama 'Yan Najeriya 11 Masu Damfarar Soyayya


'Yan sandan kasar Jamus
'Yan sandan kasar Jamus

A cewar sanarwar da 'yan sandan yankin Bavaria suka fitar, gungun mai lakabin bakin gatari ko Black Axe" a turance nada hannu wajen aikata manyan laifuffuka a fadin duniya inda suka fi maida hankali a damfarar ta hanyar soyayya a kasar Jamus da halasta kudaden haram.

WASHINGTON DC - A yau Laraba 'yan sandan kasar Jamus suka kama wasu mutane 11 da ake zargin mambobin wani gungun 'yan Najeriya daya kware a damfarar soyayya a wani babban samame.

'Yan sandan sun kara da cewar, "ta hanyar amfani da bayanan bogi 'yan damfarar kan gabatar da aniyar yin aure kuma idan alaka ta dore sai su rika bijiro da bukatun kudi ta sigogi daban-daban.

Hukumomin sun cigaba da cewar, a karshe sai a aika kudaden zuwa asusun ajiyar "Black Axe" dake Najeriya ta hanyar dillalan hada-hadar kudi.

Ta wannan hanya, gungun kan yi amfani da wani tsarin halasta kudaden haram da akan sayi kayan masarufin da za'a zaci na tallafi ne tare da aikewa dashi zuwa najeriya.

‘Yan sandan sun kara da cewar, a shekarar 2023 an samu rahoton damfarar soyayya har sau 450 a yankin Bavaria kawai, inda aka tafka asarar data kai ta dala milyan 7 da dubu 700.

Wadanda ake zargin, wanda dukkaninsu keda shedar zama 'yan Najeriya, na tsakanin shekaru 29 zuwa 53, an kama su ne a jiya Talata a wani samame da aka gudanar a fadin kasar.

A cewar 'yan sandan, jami'an tsaro sun yi dirar mikiya akan gine-gine 19, ciki harda gidaje da sansanonin masu neman mafaka.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG