WASHINGTON DC - Mutumin daya kafa gidauniyar darar chess a unguwannin talakawa ko “Chess in Slum” a turance, Tunde Onakoya ya dawo Najeriya inda aka yi masa tarba ta karramawa bayan daya kafa sabon tarihi a kundin bajinta na duniya a birnin New York na Amurka.
Domin samun wannan nasara, saida Onakoya ya hada gwiwa da wani zakaran wasan darar chess ba-amurke, mai suna Shawn Martinez kamar yadda kundin bajintar duniya ya bukata.
Ba wai kawai babban burin gwarzon darar chess mai shekaru 29 ya takaita ga kafa sabon tarihi bane, harma da tara dala milyaan 1 domin tallafawa ilmin yara marasa galihu.
A yayin da yake kokarin kafa sabon tarihin a dandalin Times Square, yayi haraswa sau da dama harma aka bukaci ya dakata saboda raunin lafiyarsa amma ya dage ya cigaba.
Tunde Onakoya yayi nasarar kafa sabon tarihi harma ya zarta sa’o’i 58 din daya debarwa kansa, inda da misalin karfe 12 da mintuna 40 (daidai da karfe 4 da minti 40 na asubahii agogon GMT) na ranar Asabar, 20 ga watan Afrilun da muke ciki.
Sabon mai rike da kambun bajintar yace yayi kokarin tara kudade tare da wayar da kan al’umma akan bukatar samar da damammakin karatu ga yara marasa galihu a fadin nahiyar Afrika.
Masoyin darar chess din ya samu kyakkyawar tarba a filin saukar jiragen saman Murtala Muhammad dake Legas sa’ilin daya iso Najeriya.
Masoya da magoya bayan Onakoya sun gudanar da kayataccen bikin tarbarsa, tare da raye-raye da wake-wake a filin saukar jiragen saman.
Onakoya yayi suna a tsakanin masoya wasan darar chess a duniya harma ya kafa gidauniyarsa mai taken “Chess in Slums” a turance da nufin tallafawa ilmin yara marasa galihu.
Dandalin Mu Tattauna