WASHINGTON DC - Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya dakatar da ayyuakan kamfanin jiragen saman “Dana Air” sakamakon damuwar da ake da ita game da matakansa na kiyaye afkuwar hatsari da kuma karfin jarinsa wajen gudanar da ayyuka.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren din din din a ma’aikatar, Dr. Emmanuel Meribole mai taken “dakatarwar gaggawa ga kamfanin jiragen saman Dana har sai an kammala cikakken bincike akan matakn kiyaye hatsari da karfin jarinsa.”
Wani jirgin sama mallakar kamfani, mai lamba 5N BKI, ya kauce hanyarsa a filin saukar jiragen saman murtala muhammad dake legas a safiyar jiya talata.
Sanarwar, ta umarci babban darkatan Hukumar NCAA, daya sanarda dakatar ayyukan ilahirin jiragen saman kamfanin har sai an kammala bincike.
A cewar Meribole, kamata yayi bincike ya kunshi dukkanin tsare-tsaren kiyaye afkuwar hatsari dana gudanar da gyare-gyare da kuma karfin jarin kamfanin domin tabbatar da cikakkiyar biyayya ga dokokin sufurin jiragen sama.
Dandalin Mu Tattauna