Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Isra'ila Sun Kai Hari Syria


Ministan Tsaron Isra'ila Gilad Erdan
Ministan Tsaron Isra'ila Gilad Erdan

Tun lokacin da rikicin Syria ya barke a shekarar 2011 ne dakarun Israila suke kai hari cikin Syria jefi jefi domin dakile duk wani kokarin kaiwa kungiyar Hezbollah makamai a Lebanon.

Sojojin Syria sun ce dakarun Israila sun harba nakiyoyi yau Talata da suka doshi yankin kasar a wani bangaren Arewacin Damaskas.

Sojojin sun ce sun harba wasu nakiyoyin kafin su fashe, yayin da wasu suka ruguza wani yankin da ke kusa da sansanin sojoji a Quetayfeh.

Sanarwar Sojin ta bayana cewa dakarun Syria sun harbo wani Jirgin saman Israila a wani mayar da martani

Sai dai dakarun Israila din sun ki bada wani bayani. Da ma Israila ta sha kai hare hare tun da aka fara samun tashin hankali a shekarar 2011 ba tare da fitowa fili ba.

Jami’an Israila sun tabbatar da cewa hare haren da suka kai a baya sun yi ne domin makamai masu yawa da suke zaton za a kai sansanin ‘yan ta’addar Hezbollah da ke Lebanon ne.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG