Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Amurka Sun Ce Fashewar Nashville Aikin Ne Na 'Yan Kasar Waje


Ma'aikata a Nashville
Ma'aikata a Nashville

Wata motar tafi-da-gidanka ta tarwatsa kanta a cibiyar kasuwanci ta Nashville a jihar Tennessee ta Amurka a ranar bukin Krismeti, inda mutum uku suka jikata, lamarin da ‘yan sanda suka kwatanta da aikin kasar waje.

Wata murya da aka saka a cikin motar da bata fita sosai ba na cewa bam zai tashi nan da minti 15, jim kadan kafin fashewar.

‘Yan sandan sun ce sun yi yunkurin maida martani a kan labarin bude wuta da aka ce ana yi a wurin, yayin da suka ga motar kuma suka ji muryar. Jami’an tsaron sun kwashe mutane dake kusa yayin da aka kira jami’ai masu kula da bama bamai zuwa inda fashewar ta auku.

Mai magaba da yawun ma’aikatar birnin Nashvile Don Aaron ya ce mutum uku da suka jikata a cikin fashewar an kai su asibitoci, koda yake raunukan nasu basu yi tsanani ba. Hukumomi sun ce basu iya ganewa ko akwai mutum a cikin motar tafi-da-gidankan yayin da ta tarwatse.

Hukumar kula da sha’anin jiragen sama ta dakatar da jigilar jirage na dan lokaci zuwa filin saukar jirage na Nashvile saboda batun sadarwa da fashewar ya shafa.

Mai Magana da yawun fadar White House ya fada cewa an yiwa shugaba Donald Trump bayani a kan fashewar yayin da yake hutun bukin Krismeti a jihar Florida kana za a ci gaba da shaida masa hali da ake ciki.

Shima kwamitin karbar mulki ya ce an yiwa zababben shugaban kasa Joe Biden bayani a kan fashewar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG