Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Sanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zanga a Bauchi


'Yan Sandan Najeriya a bakin aikinsu
'Yan Sandan Najeriya a bakin aikinsu

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tarwatsa tawagar wasu matasa da suka fito kan tituna suna zanga-zanga don bayyana rashin jin dadinsu kan gazawar gwamnatin jihar, wajen kammala ayyukan wasu hanya.

Da yake yi wa manema labarai bayani kan abin da ya faru, kakakin rundunar ‘yan sandan DSP Kamal Abubakar, ya ce sun sami labarin matasan sun fito suna gudanar da zanga-zanga ba tare da samun izini ba.

Hakan ya sa jami’an ‘yan sanda suka tarwatsa masu zanga-zangar tare da kama mutane biyar.

Yanzu haka dai an saki mutanen da aka kama.

Sai dai hukumomin tsaro na ganin ba laifi bane gudanar da zanga-zanga idan har an cika sharudan da aka tanadar.

A na su bangaren, jagororin matasan sun ce sun fito ne domin nunawa gwamnati rashin jin dadinsu ganin yadda aka kwashe shekaru uku da fara wasu ayyukan gina tituna, ganin irin kudaden da gwamnatin jiha ke samu.

Matasan dai na ikirarin cewa a baya sun taba sanarwa da jami’in ‘yan sanda amma kuma aka hanasu fitowa yin zanga-zangar, wanda hakan ya sa a wannan karo suka fito ba tare da neman izini ba.

Saurarin martanin da gwamnatin jihar ta Bauchi ta mayar, a wannan rahoto na Abdulwahab Muhammad:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG