Rundunar ‘Yan sandan Najeriya ta ce, dalibar makarantar Dapchi nan Leah Sharibu da ‘yan Boko Haram suka ki sako ta, tana gab da dawowa gida.
Shugaban rundunar ‘yan sandan kasar, Ibrahim Idris ne ya bayyanawa manema labarai hakan a Maiduguri, a wata ziyara da ya kai jihar Borno.
"Lallai mu na da labari, abin da mu ka tattauna ma kenan da shugaban rundunar sojin yankin." Inji Idris.
A tsakiyar makon nan ne kungiyar Boko Haram ta sako ‘yan mata dalibai na makarantar kwalejin gwamnati ta Dapchi su 105 a jihar Yobe, wata guda bayan da ta sace su.
Amma kuma bayan wata matsaya da aka cimma da kungiyar ta Boko Haram, ta sako dukkanin daliban, amma ban da Leah Sharibu ba.
Rahotannin sun nuna cewa kungiyar ta ki sakin Leah ne saboda ita ba Musulma ba ce, lamarin da ya janyo kakkausan suka daga sassan Najeriya, ciki har da kungiyoyin addinin Islama.
Sifeta Janar Idris yana rangadin wasu jihohin arewa maso gabashin kasar ne inda ya kai ziyara hedkwatar ofisoshin 'yan sandan wasu jihohin da ke yankin.
Ya kuma yaba da yadda ya ga yanayin shirin ko-ta-kwana da ya ce jami''an 'yan sandan ke ciki.
Saurari rahoton Haruna Dauda Biu domin karin bayani:
Facebook Forum