Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tattakin Neman a Sauya Dokokin Mallakar Bindiga a Amurka


Dandazon mutane da suka halarci tattakin da aka yi Washington. Ranar 24, Maris 2018
Dandazon mutane da suka halarci tattakin da aka yi Washington. Ranar 24, Maris 2018

Ana shirin gudanar da wani tattaki a Washinton, babban birnin Amurka da wasu birane a sassan duniya, inda mahalarta za su nemi a dauki matakan tsaurara mallakar bindiga domin a kawo karshen kai hare-hare a makarantu da ke haddasa mutuwar dalibai.

A yau Asabar ake sa ran dubun dubatan mutane za su halarci wani tattaki da za a yi a Washington, babban Birnin Amurka, domin jan hankulan mahukunta su dauki matakan kare rayukan dalibai a makarantu.

Taken wannan gangami shi ne March For Our Lives, wato "tattaki domin kare rayukanmu.”

Dalibai daga makarantar sakandare ta Marjory Stoneman Douglas da ke Florida ne suka hada wannan gangami, bayan da aka kashe mutane 17 a ranar 14 ga watan Fabrairu a makarantar.

Wannan kisan ta dumbin jama’a a makarantar, ita ce ta baya-bayan nan da taa auku a wata makaranta a Amurka.

Daliban, har ila yau suna nema ne da a himmatu wajen kare rayukan yara kanana a makarantu a kasar baki daya, tare da kiran da akawo karshen hare-haren bindiga da ake kai wa a makarantun.

Sama da tattaki makamancin wannan har 800 aka shirya gudanarwa a jihohin Amurka 50 da ma wasu kasashe na Duniya.

Amurkawa da dama, suna nuna turjiya wajen sadaukar da makamansu domin dakile aukuwar ire-iren wadannan hare-hare.

Sannan dan sauyin da aka samu a fannin dokokin mallakar bindiga, ba su taka-kara-sun karya ba.

Wani shirin jin ra’ayin jama’a da kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya gudanar tare da hadin gwiwar Cibiyar Bincike kan al’amuran jama’a, ya nuna cewa akwai alamun sauyi a ra’ayin Amurkawa a yanzu.

Binciken ya gano cewa, kashi 69 cikin 100 na jama’ar Amurka, na ganin ya kamata a tsaurara matakan mallakar bindiga, sabanin kashi 61 da aka gani a binciken da aka gudanar a shekarar 2016 da kuma kashi 55 a 2013.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG