Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daliban Kwalejin Da Aka Sace a Kaduna Sun Nemi Gwamnati Ta Kai Musu Dauki


Wasu daga cikin daliban da aka ceto
Wasu daga cikin daliban da aka ceto

Daliban kwalejin kula da harkokin gandun daji ta tarayya da aka sace a jihar Kaduna, sun yi kira ga gwamnati da ta cece su.

Kiran daliban ya bayyana ne a wani hoton bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta wanda ya nuna masu garkuwa da mutanen suna jibgar daliban.

“Muna kira ga gwamnati da ta zo ta cece mu, an ji wa mafi akasarinmu rauni, akwai wasunmu da suke da larura ta rashin lafiya.” Daya daga cikin daliban wanda aka nuna shi ya fada a bidiyon.

Bayani sun yi muni da cewa masu garkuwa da mutanen ne suka yi wannan bidiyo inda suka nemi a biya su miliyan 500 a matsayin kudin fansa karin su saki daliban.

A cikin bidiyon, an ji da yawa daga cikin daliban suna kira ga gwamnati da ta biya su kudaden.

A ranar Alhamis din da ta gabata, ‘yan bindigar suka abka cikin kwalejin wacce ke jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya, suka yi awon gaba da daliban.

Rahotanni sun ce sojoji sun yi dauki ba dadi da masu satar mutanen inda suka yi nasarar kubutar da dalibai 180.

Hukumomin jihar ta Kaduna sun ce sauran daliban da ‘yan bindigar suka yi nasarar guduwa da su, sun kai 39. Daga cikin daliban, 23 maza ne yayin da sauran 16 mata ne.

Hotan bidiyon dai ya nuna daliban zaune akan ganye a cikin daji, wasu daga cikin ‘yan bindigar suna dukansu da bulala.

Bidiyon ya nuna wasu daga cikin ‘yan bindigar sanyen da kayan sojoji dauke da bindigogi.

Jami’an tsaro dai sun ce suna iya bakin kokarinsu don ganin sun kubutar da daliban

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin sa kafar wandao daya da ‘yan bindigar inda ya nemi da su ajiye makamansu.

A baya-bayan nan shugaban Najeriya ya ce gwamnatinsa ba za ta yi sulhu da ‘yan bindigar.

Satar mutane don neman kudin fansa ya zama ruwan dare a Najeriya, musamman a arewaci.

A baya-bayan nan aka sako dalibai mata 279 na makarantar Jangebe na jihar Zamfara, wadanda ‘yan bindigar suka sace a makarantarsu ta kwana.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG