Zanga zangar ta samo asali ne daga kungiyar daliban makarantun kimiya da sana’ar hannu UIEPTN bayan da ta kira magoya bayan ta domin nuna bacin rai akan matsalolin da suka hada da matakin korar wasu dalibai da hukumomin ilimi suka dauka da karancin dakunan karatu da karancin malamai.
Sauran matsaloloin na su sun hada har da karancin samun karatu da rashin ban daki da dai sauransu,
Mataimakin Sakataren kungiyar dalibai ta UIEPTN Idi Mousa Uamrou ya ce shirin da suka ji daga gwamnati bayan wa’adin mako guda da suka bayar ne ya sa suka bazama akan tituna.
‘‘Cikin watan da ya wuce, tun kwanan wata na bakwai, muka fiddo matsalolnmu muka ce musu ga abinda muke so, amma mun ba da shawara a kira mu a yi shawara da mu, sai aka wayi gari wannan satin ya wuce babu wata shawara da aka yi’’ In ji Umarou .
Jami’in hulda da ‘yan jarida a makaranta Jibril Na Malka, ya ce ba za su ce uffan kan wannan matsala ba domin a cewar shi ana tattaunawa da daliban.
Wannan zanga zanga dai ta janyo arangama da tsakanin daliban da jami ;an tsaro wadanda suka yi amfani da borkonon tsohuwa wajen tarwatsa dalibai.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, zanga zangar ta bazu zuwa illahirin makarantun sakandaren birnin Yamai inda dalibai suka yi ta fashe fashe da kone konen tayoyi har da wasu motoci guda biyu.
Gwamnan Jahar Yamai Hamidu Garba, ya yi Allah wadai da wannan lamari kamar yadda za ku ji bayan kun kammala sauraron wannan rahoto da wakilin Muryar Amurka a Yamaia Souley Moumouni Bramah ya aiko mana: