'Yan Najeriyan sun ketara zuwa kasashen ne sakamakon hare-haren da kungiyar Boko Haram take kai masu ba tare da samun wani taimako ba. Wasu ma sun gudu ne a matsayin yin rigakafin hare-haren na 'yan ta'adan Boko Haram.
Wannan lamarin ya sa gwamnatin jihar Borno tana tsallakawa cikin kasashen tana kaiwa mutane taimako ganin cewa yawancin 'yan gudun hijiran 'yan asalin jihar ne. Yanzu gwamnatin ta kafa kwamitocin ta zasu kai doki wurare daban daban a kasashen musamman kasar Kamaru da tafi yawan mutane.
Abdulrahaman Abdulkarim yana daya daga cikin 'yan kwamitin da gwamnati ta kafa domin tallafawa mutanen da suke cikin kasar Kamru kusa da iyaka da Najeriya kamar garin Fotokwal. Yanzu sun kai kaya domin taimakawa mutanen dake Kamaru.
Wani Malam Abacha Bulunkutu wanda ya tsere zuwa Kamaru ya bayyana irin halin da suke ciki a garin Fotokwal. Da farko sun sha wuya amma tunda gwamna Ibrahim Shettima ya aiko masu da doki sun samu sassaucin abinci da kayan kwanciya. Wurin kwana ne yayi masu karanci kuma mutane suna cikin damuwa.
A lalace Malam Abacha yayi kiyasin sun kai mutum dubu bakwai a Kamaru. Suna rokon gwamnatin Najeriya ta yiwa Allah da annabinsa ta dauki matakin ganin cewa kowa ya koma gidansa.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.