Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ta'adancin Boko Haram Zai Haddasa Yunwa a Arewa Maso Gabas

Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo
Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo

Yaki tsakanin 'yan Boko Haram da sojojin Najeriya da yake kara yinkamari ya sa gwamnatocin jihohin arewa maso gabas su fara fargaban barkewar yunwa a yankinsu.

Mataimakin gwamnan jihar Borno, daya daga cikin jihohi uku dake fama da hare-haren 'yan Boko Haram, ya bayyanawa wakiliyar Muryar Amurka fargaban da suke dashi akan yiwuwar yunwa a yankinsu domin 'yan Boko Haram sun hana al'ummarsu yin noma.

A yankinsu maganar noma babu ita. A jihar Borno cikin kananan hukumomi 27 da gyar 10 da 'yan kai ke da zaman lafiya. Sauran basu da zaman lafiya. Idan damina ta wuce ba'a yi noma ba mutane ba zasu iya ciyar da kansu ba. Gwamnati kuma ba zata iya ciyar da kowa da kowa ba sai dai ta taimaka. Yace suna cikin bakin ciki da rashin sanin tabbas.

Ya kira shugaban kasa ya samar ma sojoji manyan kayan yaki da duk abubuwan da suke bukata da jiragen yaki domin a yi maza a gama yakin. Yakin bai kamata  ya kaiga haka ba.

A nashi jawabin gwamnan jihar Gombe Hassan Dankwanbo ya kira gwamnatin tarayya ta ware kudi na musamman domin sayen kayan abinci don gudun bacin rana. Sauran jihohin arewa maso gabas babu jihar da ta sayi takin da ya wuce tan dubu goma in ban da Gombe da ta sayi tan dubu ashirin. Ya kira gwamnatin tarayya ta yi kokari ta saye hatsin da jiharsa zata noma ta ajiye domin yin anfani dashi a jihohin da ba zasu iya yin noma ba. Yin hakan zai taimakawa mutanen da basu yi noma ba dasu wadanda suka noma.

To sai dai a jihar Yobe masu hada-hada a kasuwar hatsi suna kokawa da rashin samun kulawa daga gwamnatin jihar.  Lokacin sayen kaya gwamnatin jihar sai ta barsu ta je Gombe ko Kano ta sayo kayan abinci. A gaskiya gwamnatin jihar ba ta taba taimaka masu da komi ba.

Ga rahoton Sa'adatu Fawu.

Ta'adancin Boko Haram Zai Haddasa Yunwa a Arewa Maso Gabas - 3'27"

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG